Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yadda ma’aikata za su bibiyi hakkin su-hukumar kyautatuwar ma’aikata

Published

on

Babbar sakatariyar dake kula da hukumar kyautatuwar ma’aikata ta jihar kano, Hajiya Binta Fatima Salihu ta ce, babban kalubalen da suke fuskanta  shi ne al’umma ba sa zuwa kai korafi a duk lokacin da suka ci karo da wanda ya tauye musu hakkinsu.

Hajiya Binta Fatima Salihu ta bayyana hakan ne jim kadan bayan kammala shirin ‘‘Barka da Hantsi’’ na nan Freedom Radio, da ya mayar da hankali kan yadda ma’aikatan gwamnati za su rika neman hakkokinsu idan an tauye musu.

A cewar Fatima Salihu kowanne Ma’aikaci na da damar kai korafin cewa an tauye masa hakki ko kuma zargin cin zarafinsa

Haka kuma ta bayyana cewa akwai hukuncin da suke dauka kan dukkan ma’aikacin gwamnati da aka kama yana musguna wa al’umma da kuma yin wasarere da aikinsa.

Babbar sakatariyar a hukumar Kyautatuwar ma’aikata ta kuma yi kira ga dukkan sauran kungiyoyin da ke fafutukar taimakawa hukumar da su cigaba da bata gudunmawar  ta hanyar da  ta dace.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!