Labarai
FRSC: Bamu fitar da sanarwar ɗaukar ma’aikata ba
Hukumar kiyaye aukuwar haddura ta Kasa FRSC ta gargadi jama’a da su yi watsi da rade-radin da ke ta yawo a kafafen sada zumunta na internet kan cewa za’a fara aikin tantance sabin ma’aikata.
Jami’in yada labaran hukumar Bisi Kazeem, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar aka kuma rabawa manema labarai a Abuja.
A cewarsa, hukumar tana rokon masu neman aikin da sauran jama’a kan cewa su guji daukar irin wadannan maganganu marasa tushe balle makama.
Ya kara da cewa duk lokacin da aka ga irin wannan labaran za’a iya samun hukumar kai tsaye ta hanyar kiran lambar 122 don samun ingantaccen bayani, kuma kiran kyauta ne.
You must be logged in to post a comment Login