Connect with us

Labarai

An haramta kafa hanyoyin sadarwa a jihar Zamfara -CP Ayuba Elkanah  

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta haramta kafa hanyoyin sadarwa na internet ba tare da izini ba, domin inganta tsaro a jihar

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ayuba Elkanah, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya kira a Gusau.

Elkanah, ya ce bayanan da ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro suka samu sun tabbatar da cewa wasu mutane da kungiyoyi basa kiyaye matakan da hukumomi suka dauka don magance ayyukan ‘yan bindiga a jihar.

Ya ce hukumomin tsaro sun bankado wasu mutane da kungiyoyin da ba’a ba su izini ba, kuma suna kafa  hanyoyin sadarwa na internet a gidajensu da wuraren kasuwancinsu inda ake zargin ‘yan bindiga suna amfani da su.

Wannan na zuwa ne makwanni uku bayan dakatar da duk wata hanyar sadarwa ta wayar hannu a jihar da Hukumar NCC ta yi da nufin takaita sadarwa tsakanin ‘yan bindiga da ke addabar su.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!