Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Fushin zuciya: Matashi ya kashe abokinsa da almakashi

Published

on

An gurfanar da wani matashi a gaban wata kotu bisa tuhumar kashe abokinsa da almakashi.

Kotun Majistare mai lamba 35 ƙarƙashin mai sharia Huda Haruna ta gurfanar da matashin mai suna Yusuf Gambo bisa tuhumar kisan kai.

Inda Lauyar gwamnati kuma mai gabatar da kara Barista Safiya Yalwati ta roƙi kotu da a karantowa wanda ake tuhuma laifinsa nan take jami’in kotun Garba Uba ya karanto masa.

Daga nan ne mai gabatar da ƙara ta roƙi kotu da a basu wata ranar domin su sake gabatar da shi.

Ana dai zargin Yusuf Gambo da kashe abokinsa Usman da almakashi bisa wata sa’insa tsakaninsu a cikin gidan zoo.

Wakilin Freedom Radio Aminu Abdu Baka Noma ya rawaito cewar kotu ta amince da rokon Lauyar gwamnati inda ta dage zaman zuwa ranar 28 ga watan Fabrairu domin sake gabatar dashi.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!