Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

ilimi

Ganduje ya gargaɗi Kwalejin fasaha kan rashin tsafta

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta gargadi kwalejin fasaha ta jihar Kano School of Technology da ta kula da tsaftar makarantar don kiyaye lafiyar dalibai.

Kwamishinan muhalli Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan lokacin da ya kammala zagayen duban tsaftar muhalli a Kwalejin.

Ya ce “Babbar rashin tsaftar da kwalejin ta nuna a yau shi ne yadda aka bar ciyawa ta yi tsayi ba tare da an cire ta”.

“Wannan ciyawa da aka bari barazana ce ga lafiyar ɗalibai domin kuwa macizai za su iya samun mafaka a ciyawar su kuma cutar da ɗalibai”a cewar Getso.

Kwamishinan ya kuma ce “Kamata yayi a yi amfani da wannan lokaci da ɗaliban kwalejin su ke hutu wajen tsaftace muhallin amma duk da haka an samu datti a kwalejin”.

Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya buƙaci kwalejin da ta ɗauki matakin gyara kafin a sake waiwayo su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!