ilimi
Ganduje ya ruguza harkar ilimi a Kano – inji ƙungiyar masu makarantun sa kai.
Ƙungiyar masu makarantun sa kai ta jihar Kano, ta zargi gwamnatin jihar Kano da ruguza harkar ilimi wajen aiwatar da shirin ba da ilimi kyauta, kuma dole.
Shugaban kungiyar Awwalu Hussaini Ayagi, shine ya bayyana haka, jim kadan bayan kammala shirin barka da hantsi na tashar freedom rediyo da ya gudana da safiyar ranar litinin.
‘‘Ai dama wannan shirin ba da ilimi kyauta kuma dolen da gwamnatin Kano ta aiwatar, yaudara ce kawai gwamnati ta yiwa jama’a, don su rinka gani kamar taimakonsu aka yi, kuma gaskiya ba wani taimako da gwamnati ta yi sai ma rugurguza harkar ilimi’’
‘‘Shi ya sa yanzu mu ke son jan hankalin jama’a kar su saki jiki cewa, yanzu gwamnati ta bai wa yayansu ilimi kyauta su ki taimakawa yayansu, wannan shine illar ilimi kyauta, shine ma yasa yara suke ta faduwa a jarrabawa’’
‘‘Yanzu dubi kamar wanann jarrabawar ta qualifying din nan da dalibai su ka fadi a kwanan nan, duk matasalar ilimi kyauta ta janyo’’ a cewar shugaban kungiyar masu makarantun sa kai ta jihar Kano.
‘‘Yanzu akwai wani jami’in gwmanati da ya zo nan gidan rediyon, ku ka tattauna da shi a kwanakin baya, ya ke cewa, wai, gwamnati tana ba da abinci da littafi da tufafi kyauta ga yara, yanzu a nuna mini wata makaranta anan Kano guda daya wadda gwamnati ta ke ba da abinci da tufafi da litattafai ga yara kyauta’’? Inji Ayagi.
You must be logged in to post a comment Login