Labarai
Ganduje zai samar da motocin sufuri a Kano
Gwamnatin jihar Kano ta ce, za ta sayo motoci masu daukar mutum 56 guda ɗari domin rage cinkoson ababen hawa.
Kwamishinan harkokin Sufuri Mahmud Muhammad Santsi ne ya bayyana hakan a wajen buɗe taron masu ruwa da tsaki akan harkokin Sufuri.
Mahmud Santsi ya ce, “ba iya kano kadai ake fama da cunkoson ababen hawa ba duk Najeriya ne, domin kuwa yawan ababen hawa na haifar da cunkosonsu akan titi, duk da kokarin da gwamnati ke yi, wannan ne ya sa muka fito da tsarin da zai inganta harkokin sufuri”.
“Gwamanti za ta samar da wata hukuma ta musamman tare da samar da dokoki da za su tabbatar da an tsara harkokin sufuri a Kano don rage cunkoso.
Mahmud Santsi ya ƙara da cewa, a yanzu gwamnati ta mayar da hankali wajen gina hanyoyi don samun saukin cunkoson ababen hawa.
“Yanzu haka gwamna Ganduje ya sahale mana mu siyo motoci masu daukar mutum 56 guda ɗari domin fara harkokin Sufuri a jihar” a cewar Santsi.
You must be logged in to post a comment Login