Labarai
Garba Shehu ya ƙaryata Jonathan kan kalamansa ga Buhari

Tsohon mai bai wa marigayi shugaba Muhammadu Buhari shawara a harkokin yaɗa labarai Garba Shehu, ya karyata iƙirarin tsohon Shugaban ƙasa Goodluck Jonathan cewa, ƙungiyar Boko Haram ta taɓa naɗa Buhari a matsayin wanda zai jagoranci tattaunawar sulhu tsakaninsu da Gwamnatin Tarayya.
Garba Shehu ya yi wannan raddi ne a cikin wata sanarwa da ya fitar mai taken “Boko Haram ba su taɓa naɗa Buhari a matsayin mai shiga tsakani ba.”
Wannan martani na Garba Shehu, ya biyo bayan jawabin Jonathan a wajen kaddamar da littafin “Scars” da tsohon Hafsan Sojojin Najeriya, Janar Lucky Irabor mai ritaya ya rubuta.
A wajen taron, tsohon shugaban ya ce, a wani lokaci da gwamnatinsa ta kafa kwamitoci, mayakan Boko Haram sun ambaci Muhammadu Buhari a matsayin mutumin da suke so ya jagoranci tattaunawa da gwamnati.
You must be logged in to post a comment Login