Labarai
Gawar Marigayi Buhari ta isa Birnin Daura

Gawar marigayi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta isa mahaifarsa garin Daura domin yi masa jana’iza da yammacin yau Talata.
An bar filin jirgin sama na jihar Katsina ne da Gawar bayan an sauke da daga jirgin fadar shugaban kasa daga London.
Gawar marigayin, bar filin jirgin tare da rakiyar shugaba Tinubu, da mataimakinsa Kashim Shettima, da uwargidan marigayin, Aisha Buhari da kuma wasu daga cikin yaransa.
BBC ta ruwaito cewa, za a gudanar da sallar jana’iza sannan a binne marigayin a cikin gidansa.
You must be logged in to post a comment Login