Labarai
Gawar marigayi Muhammadu Buhari ta isa jihar Katsina

Gawar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta isa filin jirgin sama na Umaru Musa YarAdua da ke jihar Katsina bisa rakiyar mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima.
Marigayi shugaba Muhammadu Buhari ya rasu ne a ranar 13 ga watan Yulin 2025 a wani asibiti da ke Landan bayan rashin lafiya, kuma ya rasu ne yana da shekara 82.
Kafar BBC ta ruwaito cewa, za a wuce da gawar tasa ne zuwa mahaifa marigayin garin Daura domin yi masa jana’iza a cikin gidansa.
You must be logged in to post a comment Login