Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

‘yan bindiga sun harbe shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Ideato ta Arewa

Published

on

Wasu ‘yan bindiga sun harbe shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Ideato ta Arewa da ke jihar Imo wato Sunny Ejiagwu da safiyar yau Juma’a.

Ejiagwu wanda aka fi sani da Ohaneze na daya daga cikin shugabannin jam’iyyar APCn na kananan hukumomi ashirin da bakwai da shugaban jam’iyya na jihar ta Imo Daniel Nwafor ya kaddamar da su ranar Litinin din da ta gabata, bayan da jam’iyyar ta dage ranar zaben shugabannin ta a jihar kamar yadda wata kotu ta bayar da umarnin hakan.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Dasuki Galadanci wanda ya tabbatar da faruwar al’amarin ga manema labarai, yace yanzu haka an mika gawar mamacin zuwa dakin ajiye gawarwaki da ke Owerri.

A cewar kwamishinan ‘yan sandan shugaban jam’iyyar APCn na karamar hukumar Ideato ta arewa ‘yan bindigar sun kashe shi ne akan hanyar Akwokwa, lokacin da yake hanyar sa ta zuwa gida.

Ya kara da cewa tuni rundunar ‘yan sandan jihar ta bayar da umarnin gudanar da bincike kan wannan al’amari, tare da kamo wadanda ke da hannu wajen aikata kisan, domin gurfanar da su gaban kuliya.

Da yake zantawa da manema labara, shugaban jam’iyyar PAC na jihar ta Imo yayi All— wadai da wannan danyan aikin da batan garin suka yi, tare d kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da bindike kan wannan al’amari, kasancewar hakan barazana ce ga tsaron jihar da ma kasa baki daya.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!