Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Shugaba Buhari ya aika sunan Farfesa Bolaji Owasanoye a massayin shugaba hukumar ICPC

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aikewa Majalisar Dattijai wasikar neman tabbatar da Farfesa Bolaji Owasanoye a matsayin shugaban hukumar nan mai yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC tare da Mambobin hukumar guda takwas.

Shugababan Majalisar ta Dattijai Sanata Bukola Saraki ne ya karanto wasikar a zaman Majalisar na jiya Talata.

Baya ga Farfesa Bolaji Owasanoye da shugaban ya na nemi a tabbatar a maysayin shugaban hukumar ta ICPC, akwai mambobi 8 da su ka hadar Dokta Grace Chinda daga Jihar Delta da Okolo Titus daga Jihar Enugu, sai Obiora Ugwedebia daga Jihar Anambra.

Sauran su ne Misis Olubukola Balogun daga Jihar Lagos da Justice Adamu Muhammad daga Jihar Katsina da Hannatu Muhammad daga Jihar Jigawa, sai Abdullahi Maikano Sa’idu daga Jihar Niger da kuma Yahaya Umar Dauda daga Jihar Nasarawa.

Sai dai a jiya Talata ne Majalisar ta tafi hutu har sai ranar 25 ga watan Satumba mai zuwa za ta dawo zama.

Wanda hakan ke nuni da cewa tabbatar da jami’an ba zai yi wu ba har sai bayan dawowarta.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!