Labarai
Gidaje 200 zuwa 300 ne ke rushewa a Najeriya duk shekara- COREN

Majalisar kula da ayyukan Injiniyoyi ta kasa COREN ta ce zata rufe duk wani guri da ake aikin daya saba dokar ta tare da mika Injiniyan a gaban Kotu domin dakile illar rushewar Gine – Ginen dake sanadin mutuwar al’ummar kasa.
Shugaban Majalisar Injiniya Farfesa Sadik Zubair Abubakar, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da Majalisar ta COREN ta gudanar a nan Kano.
Shugaban ya ce, shekaru 53 kenan da kafa COREN amma kwalliya bata biya kudin Sabulu ba, domin a iya Abuja majalisar take aiki wanda hakan yasa suke so su rika yin aiki a kowacce jiha a Najeriya a halin yanzu.
Ya kara da cewa a binciken da COREN ta gudanar ta gano cewa kimanin gidaje dari biyu zuwa dari uku ne suke rushewa a Najeriya a duk shekara a don haka ya zama wajibi a sauya wannan tsari.
Majalisar ta bada lambar waya da mutane zasu kwarmata duk wani aikin Injiniya da suka gano ana tafka Almundahana kuma za a bada kyauta ga masu kwarmata wa.
You must be logged in to post a comment Login