Kimiyya
Gine-gine barkatai: Rashin bin doka da oda ne ke tasiri a Najeriya -Ɗan Najeriya mazaunin Amurka
Malami a sashin kimiyyar sinadarai a jami’ar Arlington da ke birnin Texas a kasar Amurka ya ce, rashin bin doka da tsari ne yasa ake yin gini Barkatai a Najeriya.
Malamin wanda mai sharhi ne kan al’amuran yau da kullum ɗan asalin jihar Kano mazaunin Texas Fahad Ibrahim Ɗanladi ya ce “ƙasashen yamma ba bada bari ayi gini ba tare da lasisin mahukunta ba”.
Ya ci gaba da cewa “A irin waɗannan ƙasashen ba inda ake ganin kwata akan hanya ko sokawe ya fito waje”.
Fahad Ibrahim Ɗanladi ya ce dole mazaunin irin waɗannan ƙasashen su riƙa tsafatace gidajen su kamar yadda dokar su ta ke.
Sai dai ya yi kira ga mahukunta a Najeriya da su ɗauki irin waɗannan dokiki domin tsaftace ƙasar.
You must be logged in to post a comment Login