Labarai
Kungiyar tsofaffun daliban Sakandaren Gwale Goba Aji na 1994 ta samar da littafai ga daliban makarantar
Wasu daga cikin tsofaffun daliban sakandaren Gwale Goba, sun samar da tallafin Littattafai guda dubu daya da dari Tara.
Mutanan da suka samar da littattafan sun hadar da Barrister Sunusi Musa SAN da Alhaji Nasir Miqdad.
An mika litattafan ga mahukuntan sakandaren ta Gwale a ranar Laraba 22 ga watan Janairun shekarar 2025.
Da yake jawabi yayin mika littattafan Alhaji Bello Danbaffa ya yi godiya ga Allah da ya basu Ikon halartar taron mai mutukar muhimmanci sannan ya jawo hankali daliban makarantar kan su dage suma suyi sama da abinda sukewa makarantar na Tallafi.
Shi kuwa shugaban kungiyar daliban makarantar Gobna na kasa yabawa tsoffin daliban makarantar ya yi ‘yan Aji na 1994 kan irin taimakon da sukewa makarantar.
Shi kuwa shugaan sakandaren ta Gwale nuna jin dadinsa ya yi dangane da tallafin Littafan da suka kawo makarantar.
Ya kuma ce kusan dukkanin abubuwan da ake amfani dasu a makarantar GOBA ce ta samar dasu.
Ya kuma koka kan rashin tsaro da makarantar ke fama dashi, da rashin motar makaranta.
A karshe a raba littattafan ga daliban, sannan suka gayyaci malamin su wanda yake shugaban makarantar GAC Gwale ne, wato Malam Shehu Bako ya tofa albarkacin bakinsa, inda yake cewa shifa bashi da daliban da yake alfahari dasu irin Class 94.
Wadan da suka halarci taron sun hadar da:
1. Bello Danbaffa shugaba
2. Magaji Sabo Kabara magatakardar
3. Muhammad Auwal
4. Ya’u Shehu
5. Baba Shehu
6. Nura Lawan
7. Mudassir Yusuf Ibrahim jami’in yada labarai.
You must be logged in to post a comment Login