Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gobara ta ƙone wani mutum guda a ma’aikatar ilimi ta tarayya

Published

on

Hukumar kashe gobara a babban birnin tarayya Abuja ta tabbatar da ƙonewar mutum 1 sakamakon gobarar da ta tashi a ma’aikatar ilimi ta tarayya.

Mai magana da yawun hukumar Ibrahim Muhammad ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai.

Ya ce har yanzu ba’a kai ga gano musabbabin tashin gobarar ba,sai dai ya ce gobarar ta tashi da yammacin ranar L       araba a sakatariyar Abuja.

A cewarsa wutar ta ƙone ƙafafuwan mutumin da ba a kai ga bayyana sunan sa ba, a ƙoƙarinsa na fita bayan kammala aikin sa na wannan rana.

Ibrahim Muhammad ya ce, gobarar ta shafi bankin da ke Zenith da ke maƙwabtaka da sakatariyar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!