Connect with us

Manyan Labarai

Gobara ta tashi a gidan dan majalisar wakalai na jihar Zamfara

Published

on

Hukumar kashe gobara ta jihar Zamfara ta tabbatar da faruwar wata gobata a gidan dan majalisar wakilai Kabir Mai-palace mai wakiltar Gasau da Tsafe ta jihar ta Zamfara.

 

Mataimakin darakta  kiyayye  gobara da wayar da kan al’umma a hukumar kashe gobarar Abdullahi Jibo   ne ya bayyanawa kamfanin dillacin labarai na kasa NAN.

 

Abdullahi Jibo ya ce annobar wanda ya tashi a gidan dan majalisar wakilan da ke Anguwar Yarima a garin Gusau , ake kuma kyautata zaton cewa wutar ta faru ne sakamakon kawo wutar lantarki.

 

Ya kara da cewar hukumar ta samu kiran waya ne da misalin karfe 10:30 na safe, inda tuni suka aike da ma’aikatansu domin shawo kan gobarar.

 

Kawo yanzu dai babu wanda ya samu rauni sakamakon gobarar, inda aka samu nasarar fito da motoci guda biyu a gidan.

 

Daraktan ya ja hankalin mazauna jihar Zamfara da su tabbata sun kula da kashe na’urorin lantarki, sannan su tabbata sun sanar da hukuma da zarar an samu wata matsala ta gobara.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,692 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!