Connect with us

Labaran Kano

Majalisar dokokin Kano ta tsige shugaban masu rinjaye

Published

on

Majalisar dokokin jihar Kano ta tsige shugaban masu rinjaye na majalisar Abdul Labaran Madari.

Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin gaggawa da Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Bunkure Muhammed Uba  Gurjiya ya gabatar yayin zaman majalisar da safiyar nan.

Majalisar ta Kuma zabi mataimakin shugaban majalisar Kabiru Hassan Dashi da ya zama sabon shugaban masu rinjaye na majalisar, yayin da mamba mai wakiltar karamar hukumar Munjibir Tasi’u Ibrahim Zabaina ya zama sabon mataimakin shugaban masu rinjaye na majalisar.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,797 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!