Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Kano-Gobara ta tashi sau 7

Published

on

Wata gobara ta tashi har sau 7 a rana guda a wani gida dake unguwar Kofar Nasarawa bayan jami’ar Yusuf Maitama Sule.

A zantawar mu da wata Dattijiwa mai suna Hauwa Mai Kaji, ta ce jikan ta mai suna Muhammad wanda aka fi sani da Daddy shine ya tako Dan Aljannu a kan hanya a lokacin da yake guje-guje a ranar Juma’a wanda ya sha alwashi sai ya rama abin da yaron ya yi masu.

Ta kuma ce hatta katifar da suka kwanta sai da wuta ta tashi akai kuma komai na gidan ya kone.

Mun zanta da Daddy mai shekaru 10 ya ce kullum sai an daga shi sama a damafara shi a kasa sannan Kuma a dauke shi a Kai shi wani wuri inda yake gane-ganen Aljannu masu kaho.

Wakilin mu Tijjani Adamu ya rawaito  cewa yanzu haka wuta ta cinye kayan gidan baki daya inda mutane suke shiga zuwa jaje tare da rusa kukan ban tausayi.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!