Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Guarantee Radio ta sha da kyar a hannun Freedom Radio

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Guarantee Radio ta sha da kyar a hannun takwararta ta Freedom a wani wasan sada zumunci aka fafata a yammancin juma’ar nan.

Wasan wanda aka shirya da nufin murnar auren Shugaban Sashen Shirye-shiryen na Guarantee Radio Suyudi Isa Jibril Bichi ya gudana ne a filin wasa na Freedom Radio Arena dake harabar Freedom Radio.

Yan wasan Freedom Radio a yayin gabatar da wasan

Freedom Radio ce ta fara zura kwallo a wasan ta hannun Enjiniya Zahraddin kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Sai dai ana dab da tashi daga wasan ne Guarantee Radio ta farke kwallon ta hannun dan wasan bayan ta Kamalu.

Wasu jama’a jim kadan bayan kammala wasan

A karshe an tashi daga wasa cancaras wato daya da daya.

Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala wasan Kyaftin din Guarantee Radio Anas Sani Tukuntawa ya zargi alkalin wasa da nuna bangaranci, inda ya yi ikirarin cewa sun samu bugun daga kai sai mai tsaron raga amma alkalin ya hana.

Sai dai alkalin wasan Tijjani Alfindiki ya musanta zargin inda ya bayyana cewa ya kamanta adalci dai-dai gwargwado a wasan.

Shi kuwa Kyaftin din Freedom Radio Nasir Salisu Zango ya zargi Guarantee Radio da zuba sojojin haya, zargin da Coach din Guarantee Radio Abubakar Sadiq ya musanta, yana mai cewa gaba daya wadanda suka buga wasan ma’aikatansu ne.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!