Labarai
Gudanar da managartan ayyuka na kan Injiniyoyi- Kwamishinan ayyuka na Kano
Kwamishinan ayyuka da gidaje na jihar Kano, Injiniya Mu’azu Magaji ya bayyana cewa hakkin gudanar da managartan ayyuka da za su ciyar da kasar nan gaba musamman a fannin kere-kere da gine-gine ya ratayu ne a wuyan injiniyoyi.
Kwamashinan ya bayyana haka ne a wajen taron da tsofaffin daliban tsangayar horar da injiniyoyi ta Jami’ar Bayero suka shirya don tattauna hanyoyin bunkasa karatun injiniya a kasar nan.
Ya ce wajibi ne gwamnatoci a ko wane mataki a kasar nan su kara kokarin bunkasa karatun aikin injiniya ta yadda zai kasance suna gudanar da ayyukan kere-kere a Najeriya ba tare da la’akari da na kasashen ketare ba.
A jawabinsa, shugaban Jami’ar Bayero, Farfesa Muhammad Yahuza Bello wanda shugaban tsangayar horar da injiniyoyi na Jamiar, Farfesa Salisu Dan’azumi ya wakilta, cewa ya yi yana da kyau tsofaffin dalibai su rinka waiwayar makarantun da suka kammala don ba su dukkan gudunmawar da ta dace, don ta hakan ne ‘yan baya za su samu fa’idar lamarin.
Wakilin mu Abubakar Tijani Rabi’u ya ruwaito cewa an karrama wasu ‘ya’yan kungiyar saboda irin kokarin da suke yi na ciyar da aikin injiniya gaba a kasar nan.