Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Injiniyoyi nada rawar takawa wajen kawowa Kasar nan cigaba-Sarkin Bichi

Published

on

 

Mai Martaba Sarkin Bichi Alh Dr Nasir Ado Bayero yace injiniyoyi nada Mahimmiyar rawar takawa wajan cigaban Nijeriya dama duniya bakin daya saboda sana’a ce mai mutukar mahimmanci ga al’ummar.

 

Alh Dr Nasir Ado Bayero yace zaman Injiniya Mustapha Balarabe Shugaban Kungiyar Injiniyoyi na duniya abun alfahari ga duk wani dan jihar Kano da bakaken fata bakin daya.

 

Sarki ya horin sabon Shugaban Kungiyar Injiniyoyi na duniya Injiniya Mustapha Balarabe daya kawo abubawan da zasu ciyar da jihar Kano da Nijeriya baki daya gaba domin mukamin daya samun mikamine Wanda zai rika yi mu’amula da al’ummar duniya kala kala.

 

A Jawabinsa Shugaban Kungiyar Injiniyoyi na duniya Injiniya Mustapha Balarabe yace ya je fadar Sarkin domin sanar da shi mukami daya samun na Shugabanci Kungiyar Injiniyoyi na duniya da kuma yiwa sarki Ta’aziyar rasuwar yar uwar Hajiya Hauwa Ado Bayero.

 

Injiniyoyi Mustapha ya godewar Sarkin bisa bawa daya daga cikin Yan Kungiyar Injiniyoyi na Kasa Sarauta Injiniya Murtala Mukkadas tare da tarbatarwa Sarkin zama jakada na garin.

 

Tun da farko Shugaban Kungiyar Injiniyoyi na Jahar Kano Injiniya Ibrahim Usman Dederi yace sun je fadarsa Sarkin da Bichi domin Kyautata alaka Kungiyar da Masarautar Bichi da kuma gabatar daya daga cikin yan jihar Kano Injiniya Mustapha Balarabe Wanda ya zaman Shugaban Kungiyar Injiniyoyi na duniya domin neman goyon bayan dasa Albarka.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!