Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamna Abba Gida-gida ya ƙaddamar da fara aikin tal’udu

Published

on

Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar da fara aikin gadar sama da ƙasa da a shataletalen tal’udu dake ƙaramar hukumar Gwale.

Da yake jawabi a wajen kaddamar da aikin gadar, gwamna Abba Kabir Yusuf yace samar da katafariyar gadar zai saukakawa al’ummar dake bin hanyar wahalhalun sufuri da cunkoso da ake fuskanta.

Kazalika ya ce gwamnati zata sanya idanu wajen ganin an kammala aikin cikin ƙanƙanin lokaci wanda yasa gwamnati ta tanadi duk wasu kayan aiki da ake buƙata domin kammala aikin hanzari.

Yace an bada aikin gadar ga nagartaccen Kamfani domin yin aiki mai inganci wanda kuma za a kammala shi cikin ƙanƙanin lokaci.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kara da cewa yanzu haka gwamnatinsa ta shirya tsaf domin bayar da tallafi ga matasa domin samar musu da hanyoyin sana’o’in dogaro da kai.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!