Labarai
Gwamna Abba Gida-gida ya bada tallafin kayan abinci ga ma’aikatan gidan gwamnati
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bayar da tallafin kayan abinci na miliyoyin Naira ga ma’aikatan gidan gwamnatin da ke aiki tare da shi a wani ɓangare na watan Ramadan.
Wannan na ƙunshe ta cikin wata takarda mai ɗauke da sa hannun Babban Daraktan yaɗa labaran Gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Lahadi.
A cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin abincin sun haɗar daga matakin aiki na 1 zuwa na 12 kayan da aka basu sun haɗar da buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 50, da katon macaroni, sai buhun gero mai kwano 10, da kuma kudi N10,000 kowanne.
Da yake gabatar da kayayyakin cikin yanayi na musamman, gwamnan ya bayyana godiyarsa ga Allah da ya ba shi damar yin hakan da nufin ganin an samu nasara ga ma’aikatan sa a cikin watan Ramadan mai albarka.
“Yau rana ce ta Musamman a gare ni har ma’aikata na a gidan gwamnati domin na fara cika alkawuran yakin neman zabe da na inganta ayyukan jin dadi ga ma’aikatan gwamnati.” a cewar Gwamnan.
Gwamnan ya ci gaba da bayyana cewa za a ci gaba da gudanar da wasu ayyuka na alheri ga ma’aikatan musamman idan suka tsaya tsayin daka a kan ayyukan su na daidai.
“Dangantaka ta da ku ba ta siyasa ba ce don haka za ku iya yin ra’ayoyinku daban-daban, amma abin da nake bukata daga gare ku shi ne sadaukarwa, aiki tukuru, da addu’a domin mu cimma abin da muke a nan.”
Daga nan sai ya yi kira gare su da su yi amfani da watan Ramadan ta hanyar yawaita ayyukan ibada tare da yin addu’a ga gwamnati da kasa baki daya Allah ya kawo mana dauki, musamman a wannan lokaci na matsin rayuwa.
Tun da farko mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya yabawa gwamnan bisa wannan karamcin da ya nuna, inda ya bayyana hakan a matsayin irinsa da aka taba samu a jihar.
Kwamared Abdussalam ya yi kira ga wadanda suka ci gajiyar shirin da su maida hankali wajen sadaukar da ayyukansu, rikon amana, da addu’a ga gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf.
You must be logged in to post a comment Login