Connect with us

Labarai

Covid-19: Tallafawa mabukaci ba lallai sai mai kudi ba-Mukyautata Rayuwa

Published

on

Gidauniyar Mukyautata Rayuwa, dake nan Kano, ta sha alwashin ci gaba da tallafawa mutanan da basu dashi musamman iyayan da aka mutu aka bar musu marayu a wannann lokaci na Azumin watan Ramadan da al’umma ke zaman gida sanadiyyar annobar Corona.

Shugaban Gidauniyar Malam, Shehu Baba Yaro, ne ya bayyana hakan yayin da yake mika tallafin kayan abinci ga iyayen marayun da iyayan su suka rasu suka barsu domin rage musu radadin da ake ciki na babu a wananan lokacin.

Malam Baba Yaro, ya kuma ce duk wanda ya taimakawa wanda bashi da shi a wannan lokaci da kayan abinci zai samu lada mai yawa a wajen Allah Subhanawu-wata’ala.

Ya kuma shawarci masu hannu da shuni da su daure wajen taimakawa wadan da basu da shi domin samun rabauta a nan gidan Duniya dama gobe kiyama.

Ya kuma ce ‘ya’yan kungiyar ne sukai karo karo don tallafawa iyayan marayu  da suka fito daga sassa daban daban a fadin Jihar ta Kano.

Ya kara da cewa dole sai mutane sun daure wajen aikata al’khairi domin kuwa shaidan yana sanya shakku a zuciyar duk wanda yaso gudanar da alkhairin.

Baba Yaro ya ce “ba lallai sai mai arziki ne zai taimakawa wadan da basu dashi ba” a cewar sa” shima wanda yake da rufin asiri dai dai gwargwado zai iya taimakawa wanda bashi dashi domin rabauta a gurin Allah Subhanawu wata’ala.

Wasu daga cikin mutanan da suka amfana da tallafin kayan abincin da suka fito daga sassa daban daban na jihar Kano sun bayyan farin cikin su, inda suka godewa kungiyar bisa tallafin kayan abincin data basu domin sanya farin cikin a zukatan su.

Covid-19: Ganduje ya amince a gudanar da sallar idi a Kano

Covid-19: An baiwa gwamnatin Jigawa tallafin kayan abinci kan Corona

Gidauniyar ta Mukyautata Rayuwa, dai ta tallafawa iyayan marayun da tallafin karamin buhun Shinkafa da Taliya da Man Girki da Sikari da dai sauran su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Coronavirus

Covid-19: El-rufa’i ya kara tsawaita dokar kulle a Kaduna

Published

on

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-rufai ya kara tsawaita dokar kulle da zaman gida tsawon makonni biyu a jihar.

Mataimakiyar gwamnan jihar Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe ce ta bayyana hakan, cikin wata sanarwa da fitar a yammacin Talatar nan wanda ta ce gwamnati ta tsawaita dokar kulle da zaman gida a jihar ne domin dakile cutar Corona.

Sanarwar ta bukaci al’ummar jihar ta Kaduna da su cigaba da daukar matakan kariya da masana kiwon lafiya suka gindaya na sanya takunkumin rufe baki da hanci, da yawaita wanke hannu da kuma bada tazara a tsakanin juna, sannan al’umma su kaucewa taron jama’a masu yawa.

Haka kuma gwamnatin jihar ta ce a yanzu al’umma za su rika sararawa a ranaku guda uku a jere cikin mako ranakun sune, ranar Talata Laraba da kuma ranar Alhamis.

Kananan wuraren kasuwanci da aka amince su bude za su rika fitowa a wadannnan ranaku daga karfe 10 na safe zuwa 4 na yamma.
Su kuwa jama’a masu zirga-zirga za su rika fita ne daga karfe 6 na safe zuwa 6 na yamma a ranakun.

Har ila yau gwamnatin Kaduna ta gargadi ‘yan kasuwannin da ba a amince musu su bude ba, kan suyi biyayya da dokokin da aka sanya.

Har ila yau, sanarwar ta kara da cewa kotun tafi da gidanka zata cigaba da ayyukanta domin hukunta masu karya dokoki da kuma masu yawon dare a yayin dokar kullen.

Haka kuma gwamnatin Kaduna tace makarantu da wuraren ibadu dukkansu za su cigaba da zama a kulle.

Sanarwar tace yanzu haka jihar Kaduna ta yiwa mutane dubu daya da dari tara (1900) gwajin cutar Corona inda ta samu mutane 189 dake dauke da cutar.

A karshe gwamnatin Kaduna ta ce cikin wannan karin makonni biyu zata mayar da hankali wajen kara habaka ayyukanta na yaki da cutar Coronavirus.

*BS*

Continue Reading

Coronavirus

‘Yan kasuwa sun nemi Ganduje ya bude Kasuwanni sau biyu a mako

Published

on

‘Yan Kasuwa sun  bukaci gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da ya duba dokar kulle na zaman gida tare da bada dama ga ‘yan Kasuwannin Sabongari da Kwari da na  Singer domin fitowa Kasuwancin su a kebabbun ranakun  da aka ware a mako don gudanar da nasu Kasuwancin.

Alhaji Imamu Tafida, Tafidan Dakayyawa kuma daya daga cikin Dattijan Kasuwar Muhammad Abubakar Rimi, wato Sabongari shi ne yayi wannan kira duba da mawuyacin halin da ‘yan Kasuwan suke ciki kamar yadda jagororin  Kasuwar suka tabbatar.

Alhaji Imamu Tafida, ya ce ‘yan kasuwa da dama, sun tafka asara ta miliyoyin nairori sakamakon rufe kasuwannin, kasancewar kayan da suka siyo basu shigo ba dalilin hana shige da fice, hakazalika wanda ake dasu a kasuwar ba a siyar dasu ba.

Tafidan Dakayyawan, ya kuma bada tabbaci ga gwamnati na cewar zasu yi duk mai yiwuwa wajen daukar matakan kariya daga cutar ta Corona daga bangaren su da masu mu’amala dasu da zarar an basu damar gudanar da Kasuwancin su.

Wakilin mu, Aminu Halilu Tudunwada, ya ruwaito mana cewa, Alhaji Imamu Tafida, ya bukaci al’umma dasu bi umarnin hukumomi da ma’aikatan lafiya, tare da rubanya addu’a domin ganin an kawar da wannan annoba da ta kawo tsaiko a al’amuran yau da kullum na jama’a.

Continue Reading

Coronavirus

Nijar: An fara feshin magani kan Corona a makarantu

Published

on

Hukumomin a jahar Damagaram sun kaddamar da fara feshin maganin rigakafin Covid-19 a cikin makarantun boko

A sadiyar Litinin dinnan ne shugaban kwamitin yaki da wannan cuta kuma magatakardar fadar gwamnan jihar Damagaram ya jagoranci bikin kaddamar da feshin a cikin makarantar Mela Douaram da ke tsakiyar birnin na Damagaram.

Magatakardar ya bayyana cewa sun fara wannan aiki ne a wani mataki na kare daliban daga kamuwa da wannan cuta ta Covid-19.

Wakilin mu Yakubu Umar Mai Gizawa ya rawaito mana cewa tun a kwanakin baya ne dai gwamnati ta sanar da ranar daya ga watan Yuni mai zuwa a matsayin ranar ranar da za’a koma bakin ajijuwan makarantun bayan shafe tsawan lokaci suna rufe sakamakon yaki da ake da cutar Covid-19.

Labarai masu alaka:

Amsoshin tambayoyi 20 kan cutar Corona – Dr. Ibrahim Musa

Covid-19: Gwamnati ta bada damar cigaba da sufuri a Nijar

Continue Reading

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 324,535 other subscribers.

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!