Labarai
Gwamna Abba Kabir ya bada umarnin tantance Malaman BESDA

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya umarci hukumar Ilimin bai daya ta jiha SUBEB da ta fara tantance malaimai da ke koyarwa a tsarin nan na BESDA domin daukar wadanda suka cancanta a matsayin cikakkun ma’aikatan gwamnati.
Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarnin ne yayin da ya ke kaddamar da rabon kayan karatu da Rubutu ga malaman Firamare da na Sakandire wanda aka gudanar a gidan gwamnati.
Haka kuma, gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya bukaci al’ummar jihar Kano da su ci gaba da tallafa wa gwamnati musamman ma a fanin Ilimi.
You must be logged in to post a comment Login