Connect with us

Labarai

Gwamna Abba Kabir ya bukaci majalisar dokoki ta yi wa dokar albashin Kansiloli Kwaskwarima

Published

on

Gwamnatin Kano ta bukaci majalisar dokokin jihar, tayi gyara akan dokar albashin zababbun kansilolin ta, domin bata damar daga darajar albashin nasu zuwa matakin da zai dace da rayuwar da ake ciki a yanzu.

 

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana bukatar hakan, lokacin da yake jawabi a wajen taron masu ruwa da tsakin kananan hukumomin jihar 44, wanda aka gudanar a fadar gwamnatin Kano.

 

Gwamna Abba ya ce, albashin da ake biyan kansilolin da suka yi mulki a shekarar 2003 lokacin Malam Ibrahim Shekarau, irin sa ake biyan kansiloli masu ci har yanzu, wanda hakan ya ke a matsayin tsantsar rashin adalci da kaskantar da su.

 

A nata jawabin, Shugabar Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomi ta Kano watau ALGON, kuma Shugabar Ƙaramar Hukumar Tudun Wada, Hajiya Sa’adatu Salisu Yusha’u Soja, ta tabbatar da cikakken haɗin kan dukkanin su ga Gwamna Abba wajen aiwatar da manufofi da shirye-shiryen gwamnati.

 

Yayin taron dai, an kuma tattauna kan batutuwan da suka shafi tsaro, kiwon lafiya, ilimi, da bunƙasa ababen more rayuwa a faɗin ƙananan hukumomi arba’in da huɗu na Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!