Connect with us

Labarai

Gwamna Abba Kabir ya kaddamar da biyan kudaden garatuti karo na 6

Published

on

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da biyan kudaden garatuti karo na shida ga tsofaffin ma’aikatan gwamnati da suka kammala aikinsu, inda aka ware kuɗi Naira biliyan 5 domin biyan su.

 

Da ya ke ƙaddamar da biyan kuɗin, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa wannan mataki na daga cikin kokarin gwamnatinsa na tabbatar da adalci da kula da walwalar ma’aikata, musamman bayan sun sadaukar da rayuwarsu wajen yi wa jihar hidima.

 

Gwamnan, Ya kara da cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da biyan hakkokin ma’aikata a kan lokaci tare da tabbatar da cewa babu wani tsohon ma’aikaci da za a bar shi cikin wahala bayan kammala aiki.

 

 Wasu daga cikin wadanda suka anfana da sun bayyana jin dadinsu, inda suka yaba wa gwamnatin jihar Kano bisa wannan kokari, inda suka ce, biyan kudaden zai taimaka musu wajen gudanar da rayuwarsu da kuma rage musu radadin halin da suke ciki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!