Labarai
Gwamna Abba Kabir ya nemi taimakon shugaba Tunibu wajen magance matsalolin tsaro

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya nemi taimakon shugaban kasa Bola Ahmad Tunibu wajen magance matsalolin tsaro da suka adabi jihar.
Hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature ya fitar da safiyar a yau Talata.
Sanarwar ta ce yayin ziyarar da gawamnan Kano ya kai fadar shugaban kasa Tinubu ya gabatar da Mahimman Abubuwan da Gwamatinsa ta sa a gaba wajen mayar da hankali musammusamn tsaro, da da abubuwan more rayuwa ga al’ummar jihar Kano.
You must be logged in to post a comment Login