Labarai
Gwamna Abba Kabir ya sanya hannu kan dokar samar da karin hukumomi 4

Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya sanya hannu kan dokar samar da wasu sabbin hukumomi guda huɗu.
Babban daraktan yaɗa labaran gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwar da ya fitar da safiyar yau Juma’a.
Sanarwar, ta ce za a samar da sabbin hukumomin ne domin kara inganta hanyoyin da za su samar wa jihar Kano ci gaba.
Sabbin hukumomin da gwamnan ya amince da samar wa sun hada da, Hukumar bayar da kariya ta jihar da Hukumar kula da Alluna da kuma tallace-tallace sai hukumar yada labarai da bunkasa fasahar sadarwa da kuma Hukumar bunkasa kanana da matsakaitan masana’antu
Haka kuma, a cewar sanarwar sanya hannu kan dokar samar da sabbin hukumomin na cikin yunƙurin gwamnatin na sabbin dabarun da za su tallafa wa kananan sana’o’i da tsaftace harkokin tallace-tallace domin bai wa al’umma kariya da kuma inganta bangaren.
You must be logged in to post a comment Login