Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamna Abba ya ƙaddamar da kwamitin bincike kan lalata dukiyar al’umma da ta gwamnati lokacin zanga-zangar lumana

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ƙaddamar da kwamitin mutune goma sha hudu da zasu gudanar da bincike kan yadda aka lalata dukiyar al’umma da na gwamnati da akayi a lokacin gudanar da zanga-zangar lumana da ta gudana a ranar 1 ga watan Agustan wannan shekarar faɗin ƙasar nan.

Gwamnan jihar Alhaji Abba Kabir Yusuf ne ya ƙaddamar da kwamitin a yau domin tabbatar da an gudanar da sahihin bincike tare da ɗaukar mataki ga duk wanda aka samu da hannu dumu-dumu wajen jagorantar lalata dukiyar al’umma da ta gwamnati.

Gwamnan ya ƙara da cewa cewa yana kira ga Wannan kwamitin da ya tabbatar ya gudanar da aikin sa na ba sani babu sabo kan duk wanda aka samu hannu komai girman sa ko mulkin sa wajen ayyana shi domin ɗaukar mataki akan sa.

Da yake jawabi shugaban kwamitin Justice Lawan Wada Muhammad ya tabbatar wa da gwamna cewa zasu gudanar da aikin su yadda ya kamata domin tabbatar da gaskiya da riƙon amana kamar yadda aka ɗora musu.

Haka kuma an bawa kwamitin wa’adin kwanaki talatin da su kammala bincike haka kuma cikin mambobin kwamitin sun haɗar da Dakta Sa’idu Ahmad Dukawa, Kwamrat Ibrahim Wayya, Alhaji Sani Asia da dai sauran

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!