Labarai
Gwamna Abba ya aikewa da majalisar dokokin Kano ƙarin sunan sabon Kwamishina

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya aikewa da majalisar dokokin jihar wasikar amincewa da naɗa Arc. Ibrahim Yakubu Adamu a matsayin Kwamishina kuma ɗaya daga cikin ƴan-majalisar zartarwa na Jihar Kano domin ci gaba da gudanar da aikin gwamnati da ci gaban Al’umma.
Da yake karanta wasika kakakin majalisar Jibrin Isma’il Falgore ya ce cikin wasikar da gwamnan ya aikewa da majalisar ta buƙaci majalisar da ta yi duba na tsanaki tare da amincewa domin tantance su a matsayin ɗaya daga ɗan majalisar zartarwa na jihar.
Arc. Ibrahim Yakubu Adamu a yanzu haka shine shugaban hukumar tsara birane ta jihar kano KNUFDa inda a yanzu gwamnan ya aike da sunan sa a matsayin wanda za’a naɗa a matsayin sabon kwamishinan kuma ɗan majalisar zartarwar gwamnatin
majalisar ta tabbatar da zata gayyato shi domin tantance shi a matsayin wanda za’a naɗa a matsayin Kwamishina.
You must be logged in to post a comment Login