Labarai
Gwamna Abba ya kafa kwamitin da zai binciki zargin Kwamishinan Sufuri kan ƙoƙarin yin belin Dillalin Ƙwayoyi

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan zargin kwamishinan sufuri na jihar Alhaji Ibrahim Namadi, kan badaƙalar yunƙurinsa na yin belin wani da ake zargi da sayar da miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Dan Wawu.
Umurnin ya biyo bayan cece-ku-ce da jama’a suka yi bayan da rahotonni suka bayyana cewa sunan Kwamishinan ya bayyana a cikin takardun karɓar belin wanda zai taimaka wajen sakin wanda ake zargin.
An bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar da safiyar yau Asabar.
Domin shawo kan lamarin Gwamna Yusuf ya kafa kwamitin bincike na musamman karkashin jagorancin Barista Aminu Hussain, mai ba shi shawara na musamman kan harkokin shari’a da tsarin mulki.
An wajabta wa kwamitin da ya bincika al’amuran da ke tattare da lamarin tare da ba da shawarar matakan da suka dace da gaggawa.
SolaceBase ta ruwaito cewa mambobin kwamitin sun hada da: Barista Aminu Hussaini a matsayin shugaba sai kuma mambobin kwamitin da suka ƙunshi Barista Hamza Haladu da Barista Hamza Nuhu Dantani da Alhaji Abdullahi Mahmoud Umar da Manjo Janar Sani Muhammad Mai ritaya sai Kwamared Kabiru Said Dakata da kuma Hajiya Bilkisu Maimota a matsayin Sakatariya.
“Yayin da ya ke sanar da kafa kwamitin, Gwamna Yusuf ya nuna matukar damuwarsa kan rashin da’a da ake zargin Wanda aka gurfanar ɗin ya na mai jaddada kudirin gwamnatinsa na yaki da shaye-shayen miyagun kwayoyi da duk wani nau’i na munanan ayyuka a jihar,” inji sanarwar.
You must be logged in to post a comment Login