Labarai
Gwamna Abba ya sha alwashin ci gaba da inganta rayuwar ma’aikata

Yayin da ake gudanar da bikin ranar ma’aikata a yau Alhamis, Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sha alwashin ci gaba da inganta rayuwar ma’aikata tare da samar musu da yanayin aiki mai kyau.
Gwamna Injiniya Abba Kabir Yusif, ya bayyana hakan ne yayin bikin ranar ma’aikata na bana da aka gudanar yau Alhamis a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar mata.
Gwamnan, ya kuma ce gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen horas da ma’aikata tare da samar musu da kayan aiki dai-dai da zamani.
A nasa jawabin, shugaban kungiyar Kwadago ta ƙasa NLC reshen jihar Kwamared Kabiru Inuwa, kira ya yi ga gwamnan kan ya cika alkawarin da ya dauka na gina dakin taro a sakatariyar kungiyar tare da sanya sunan marigayi tsohon gwamna Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi.
Yayin taron, wanda ya samu halartar kungiyoyin ma’aikata da dama da suka hadar da na gwamnati da masu zaman kansu, an karrama wasu cikin kungiyoyin ma’aikatan da suke bada gudunmawa a hukumomin da suke aiki cikin su harda kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi NULGE.
You must be logged in to post a comment Login