Labarai
Gwamna Abba ya sha alwashin hukunta waɗanda ke da hannu a rasuwa Inuwa Sharada
Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sha alwashin daukar mataki mai tsanani kan duk wanda aka samu da hannu kan zargin mutuwar shugaban rundunar masu yaƙi da kwacen Waya marigayi Inuwa Sharada, wanda ya rasu a Larabar makon nan.
Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya bayyana hakan ne yau Alhamis yayin gudanar da jana’izar marigayi Inuwa Sharada, inda ya bayyana rashin sa a matsayin abin takaici da kuma nuna rashin imani da tausayi.
Gwamna Abba ya ce, gwamnati ba za ta lamunci irin wannan abu ba, musamman ganin irin rawar da marigayin ke takawa wajen taimaka wa hukumomin tsaro da gwamnati wajen tabbatar da zaman lafiya a cikin al’umma.
Gamnan ya kuma jajanta wa iyalan marigayin da abokansa, ƴa na mai tabbatar da cewa, gwamnatin jihar Kano za ta ci gaba da tallafa musu tare da tabbatar da cewa irin wannan lamari bai sake faruwa ba a nan gaba.

You must be logged in to post a comment Login