Labarai
Gwamna Fubara da mataimakinsa za su koma bakin aiki bayan dakatarwar watanni shida

Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, tare da mataimakinsa da kuma ‘yan majalisar dokokin jihar, na shirin komawa bakin aiki daga gobe Alhamis.
Hakan na zuwa ne bayan kammala wa’adin dakatarwar watanni shida da shugaban ƙasa ya ɗora musu, sakamakon rikicin siyasa da ya kunno kai a jihar tsakanin bangarorin gwamnati.
Rahotanni sun ce matakin na shugaban ƙasa ya kasance domin saukaka tashin hankali da kuma tabbatar da zaman lafiya a harkokin mulki a jihar.
You must be logged in to post a comment Login