Labarai
Gwamna Fubara ya nemi haɗin kan al’ummar Rivers

Gwamnan jihar Rivers Siminalayi Fubara ya buƙaci al’ummar jihar da su ba shi haɗin kai wajen ciyar da jihar gaba ba tare da la’akari da bambancin siyasa ko addini ko ƙabilanci ba.
Gwamnan, ya buƙaci hakan ne yayin da ya ke jawabi ga al’ummar jihar a birnin Fatakwal.
Haka kuma, gwamna Fubara, ya gode wa Shugaba Tinubu bisa ƙoƙarin da ya ce ya yi wajen sasanta rikicin siyasar jihar.
A ranar Laraba ne Shugaba Tinubu ya sanar da kawo ƙarshen wa’adin dokar ta-ɓaci da ya sanya wa Rivers ta tsawon wata shida, sakamakon rikicin siyasar jihar da ya ƙi-ci-ƴa-ƙi-cinyewa.
Gwamnan ya ce a tsawon wata shidan da jihar ta ɗauka ƙarƙashin dokar, Tinubu ya yi ƙoƙarin sasanta duka ɓangarorin.
Fubara ya kuma ce, a yanzu shi da duka sauran ƴansiyasar jihar sun sanya jihar da muradunta a gaba domin ciyar da Rivers gaba.
You must be logged in to post a comment Login