Labarai
Gwamna Fubara ya sauke dukkanin kwamashinoni da sauran makarraban gwamnatinsa.

Gwamnan jihar Rivers Siminalayi Fubara ya sauke dukkanin kwamashinoni da sauran makarraban gwamnatinsa.
Gwamnan ya sanar da matakin ne, a yayin jawabinsa na bikin ranar ‘yancin kan Nijeriya karo na 65, inda ya jingina matakin da hukuncin kotun koli na baya -bayan nan.
Wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan Nelson Chukudi ya fitar a birnin Fatakwal a ranar Laraba, ta ce matakin ya fara aiki nan take.
You must be logged in to post a comment Login