Labarai
Gwamna Mai Mala ya bayar da umarnin daukar ‘ya’yan sojoji aiki
Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni, ya bayar da umarnin daukar ‘ya’yan sojojin da suka rasu a aiki domin tallafar rayuwar su.
Gwamnan ya bai wa Sakataren gwamnatin jihar da kuma shugaban ma’aikata umarnin bayar da takardun daukar aikin a wani bangare na bikin ranar tunawa da ‘yan mazan jiya na bana.
Haka kuma, gwamna Mai Mala Buni, ya bayar da tallafin naira miliyan Talatin a madadin gwamnatin jihar da kuma naira miliyan biyu ta kashin kansa.
Haka kuma, gwamnan, ya bukaci al’umma da suma su tallafa wa iyalan ‘yan mazan jiyan domin samun damar ci gaba da gudanar da rayuwarsu cikin sauki.
You must be logged in to post a comment Login