Labarai
Gwamna Nasir Idris ya bukaci majalisar wakilai ta binciki ayyukan Sojoji a Kebbi

Gwamnan jihar Kebbi Nasir Idris ya nuna rashin gamsuwa da tsarin da rundunar soji ke amfani da shi wajen yakar rashin tsaro yana mai kira da a sauya dabarar aiki.
Gwamman ya bayyana haka ne a ranar Litinin lokacin da ya karɓi bakuncin ‘yan Majalisar wakilai karkashin jagorancin shugaban Majalisar Tajudeen Abbas a gidan gwamnati da ke Birnin Kebbi.
Jaridar Daily Trust ta rawaito gwamnan na sake jaddada bukatar yin bincike kan janye jami’an tsaro daga makarantar ‘yan mata ta Maga mintuna kaɗan kafin ’yan bindiga su sace ’yan mata 25.
A cewar gwamnan abin mamaki ne yadda ‘yan bindiga fiye da 500 ke yawo a babura a manyan hanyoyi ba tare da an dakatar da su ba, duk da cewa gwamnati na ba da tallafi, kayan aiki, da motoci ga jami’an tsaro.
You must be logged in to post a comment Login