Labarai
Gwamna Nasiru na Kebbi ya kaddamar da tallafin kayan karatu da ababen hawa na fiye da Biliyan 2

Gwamnan jihar Kebbi ya kaddamar da rabon tallafin kayan karatu da ababen hawa na kimanin na Biliyan biyu da miliyan dari bakwai a fadin jihar.
Da ya ke magana a wajen bikin kaddamarwar a Birnin Kebbi, gwamnan ya jadda kokarin gwamnatin sa wajen bayar da ilimi mai inganci kuma kyauta, inda ya bayyana jihar Kebbin ba iya harkar noma tayi shahara har da fannin ilimi.
Daga cikin kyan da aka raba sun hadar sa Littattfan karatu da na rubutu da na’ura mai kwakwalwa da ababen hawa dan karfafa koyo da koyarwa.
Gwamnan ya bayyana wasu daga cikin nasarorin da gwamnatinsa ta samu, ciki har da gyaran makarantu sama da 2,000 tare da gina makarantu a masarautu hudu dake jihar tare da biyan Naira Biliyan Biyu na kudin makaranta ga daliban jihar.
Haka kuma, ya sanar da daukar sabbin dalibai 2,000, tare da bayar da tabbacin ci gaba da kula da walwalar malaman.
You must be logged in to post a comment Login