Labarai
Gwamna Radda ya kai wa Babban hafsan sojan ƙasa ziyara

Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya kai ziyarar aiki ga Babban Hafsan sojan kasa Laftanar Janar Olufemi Oluyede, a birnin tarayya Abuja.
Ziyarar, wadda ta mayar da hankali kan karfafa hadin gwiwa da sojoji da kuma daukar sabbin matakai don magance matsalar tsaro da ke addabar jihar.
Yayin ziyarar dai, gwamna Radda ya na tare da Babban Sakatarensa, Alhaji Abdulkadir Mamman Nasir da kuma Hajiya Hadiza Maikudi da Daraktan tsare-tsare na fadar gwamnatin Katsina sai kuma Umar Bishir, da Mataimakinsa na musamman Sabo Abba.
You must be logged in to post a comment Login