Labarai
Gwamna Umar Namadi ya jagoranci taron gwamnati da jama’a karo na 10

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi Dan modi, ya jagoranci taron gwamnati da jama’a karo na 10 a karamar hukumar Hadejia wanda ake gudanarwa a fadin jihar.
Taron ya bai wa al’ummar Hadejia damar bayyana ra’ayoyi da kuma matsalolinsu kai tsaye ga gwamna da tawagarsa, domin samun mafita da kuma kara fahimtar juna tsakanin gwamnati da jama’a.
Gwamna Dan modi ya bayyana cewa shirin zai ci gaba da zagaye dukkan sassan jihar, domin tabbatar da cewa kowa na da damar bayyana muradunsa cikin lumana.
You must be logged in to post a comment Login