Labarai
Gwamna Zulum ya kaddamar da aikin gina Titi da Gadar sama

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya kaddamar da aikin gina titi mai tsawon kilomita 7 da digo daya wanda ya tashi daga shataletalen Terminus zuwa Molai, tare da aikin ginin gadar sama, wadda ita ce gadar sama ta hudu a jihar.
Sabuwar gadar dai za ta ratsa titin Post Office ne da ke cikin birnin na Maiduguri.
Da ya ke kaddamar da aikin gwamna Zulum, ya ce, an tsara aiwatar da ayyukan ne domin magance matsalar cunkoson ababen hawa, tare da saukaka harkokin zirga-zirgar jama’a.
Haka kuma, gwamnan ya ce za a kammala aikin ne cikin watanni goma, sakamakon bayar da kwangilar kan kimanin naira biliyan 16.
Ya kuma umarci yan kwangilar da cewa, ba su da wani uzuri na bata lokaci wajen gudanar da aikin.
You must be logged in to post a comment Login