Connect with us

Labarai

Gwamnan Jihar Borno ya kai ziyara asibitin kwararru na Umaru Shehu

Published

on

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya kai ziyarar ba zata da safiyar jiya Talata a asibitin kwararru na Umaru Shehu dake birnin Maiduguri.

 

Babagana Zulum wanda ya bayyana takaicin sa ganin yadda babu wani likita koda guda daya dake bakin aikin sa a cikin asibitin a yayin zaiyarar ba zatar, sai dai ma’aikatan jinya da masu kula da marasa lafiya.

 

Rahotanni sun bayyana cewar gwamnan na Borno yayi kokarin kiran wasu daga cikin likitocin ta wayar tarho amma babu wanda ya daga.

 

Haka zalika Babagana Zulum ya bayyana rashin gamsuwar sa kan yadda ake kula da marasa lafiya a asibitin.

 

Kafin barin sa asibitin Gwamnan na jihar Borno ya bada umarnin da a baiwa babban daraktann asibitin takardar tuhuma da yayi bayani kan mai haddasa rashin likitoci a asibitin na Umaru Shehu.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,758 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!