Connect with us

Labarai

Gwamna Nasir El’Rufai ya bukaci rundunar sojin Najeriya ta tura dakaru domin dakile aikin masu satar mutane

Published

on

Gwamna Nasir El-Rufai ya bukaci rundunar sojin saman Najeriya ta tura da dakaru na samun domin dakile ayyukan masu satar mutane a titin Kaduna zuwa Abuja.

Malam Nasir El-Rufai ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke kaddamar da wasu dakarun sojojin sama da 271 wadanda aka tura su yankin karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar.

Gwamna Nasir El-Rufia ya kuma ya bawa namijin kokarin da Sarkin Birnin Gwari Alhaji Jibril Zubairu Maigwari na biyu ya yi wajen ba da fili da za a kafa barikin sojojin sama a yankin.

Ya ce turawa da sojoji zai yi matukar taimakawa wajen kawadda ayyukan batagari a jihar baki daya musamman taimakawa kokarin da dakarun Operation Dirar Mikiya da na Sharar Daji ke yi.

Malam Nasir El-Rufai ya kara da cewa, akwai bukatar rundunar ta aika da dakaru na musamman wadanda za su magance ayyukan ‘yan bindiga a jihar.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,290 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!