Labarai
Gwamnan Jihar Kano ya ƙaddamar da biyan kuɗaɗen garatuti ga tsoffin kansiloli 1,371

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da biyan kuɗaɗen garatuti ga tsoffin kansiloli 1,371 da suka yi aiki a lokacin tsohuwar gwamnati a karo na uku.
Da ya ke ƙaddamar da shirin a yau Laraba, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa matakin na daga cikin ƙudirin gwamnatinsa na cika alƙawura da kuma tabbatar da adalci ga shugabannin ƙananan hukumomi da suka taɓa hidimta wa al’umma a matsayin shugabanni.
Gwamna Abba ya kuma jaddada cewa tsoffin Kansilolin sun bayar da gagarumar gudunmawa wajen tafiyar da harkokin ƙananan hukumomi da bunƙasa ci gaban al’umma.
A cewar gwamnan, wannan shi ne karo na uku da Ya ke biyan garatuti ga tsoffin kansiloli, kuma gwamnatinsa za ta ci gaba bin wannan tsari har sai an kammala biyan dukkan waɗanda suka cancanta a faɗin ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano.
You must be logged in to post a comment Login