Labarai
Gwamnan jihar Neja ya tabbatar da ceto ƙarin ɗalibai 11 na makarantar St Mary da yan bindiga suka sace

Gwamnan jihar Neja Umar Bago ya tabbatar wa manema labarai cewa, jami’an tsaro sun ceto ƙarin ɗalibai 11 na makarantar St Mary da yan bindiga suka sace.
Gwamnan, ya bayyana cewa, an samu nasarar ceto daliban 11 ne a wani aiki na haɗin gwiwa tsakanin sojoji da yan sa kai inda aka gano yaran a wata gona
Sai dai gwamnan bai bayyana hanyoyin da aka bi wajen tantance waɗanda aka kuɓutar din ba, inda ya musanta cewa an sace yara sama da 300.
Haka kuma, ya ce, makarantar ba ta bayar da bayanan da za a iya dogara da su ba, kuma sun buɗe makarantar ne duk da gargaɗin da jami’an tsaro suka yi.
Gwamna Bago ya kara da cewa, gwamnatinsa ta buɗe wata rijista a ƙaramar hukumar Agwara domin iyaye su rubuta sunayen ƴaƴansu da suka ɓata sakamakon harin, amma zuwa yanzu iyaye 14 kacal ne suka rubuta.
You must be logged in to post a comment Login