Connect with us

Labarai

Gwamnan jihar Zamfara ya bukaci sarakunan gargajiya su gaggauta tattara rahotannin halin da tsaro ke addabar su

Published

on

Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari ya bukaci sarakunan gargajiya a jihar da su gaggauta tattara rahotannin halin da tsaro ke addabar yankunansu.

Gwamna Abdulaziz Yari ya bayyana hakan ne lokacin da yake maraba ga tawagar Sarakunan jihar wadanda suka kawo masa ziyarar barka da sallah a gidan gwamnati da ke birnin Gusau babbar birnin jihar.

Ya ce, rahoton da za su tattara ya zama wajibi ya hada da: samar da mafita da shawarwari kan yadda gwamnati za ta tunkari matsalolin tsaro da ke addabar yankunan nasu.

Gwamnan na jihar Zamfara, ya kuma ce tuni gwamnatin jihar ta fara aiki ba dare ba rana, domin tabbatar da cewa matsalolin tsaro da ke addabar jihar ya zama tarihi.

Da suke gabatar da jawabansu sarakunan Kaura Namoda dana birnin Magaji da kuma na Zurmi, Muhammad Ahmad-Asha da Hussaini Daali-Maude da kuma Abubakar Atiku sun ce za su yi duk me yiwuwa domin tabbatar da cewa an shawo kan matsalar.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,601 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!