Connect with us

Labarai

Gwamnatin Adamawa ta ayyana kwanaki 3 a matsayin ranakun zaman makokin Abdulrahman Abba

Published

on

Gwamnatin Jihar Adamawa ta ayyana kwanaki uku a matsayin ranakun zaman makoki, sakamakon mutuwar shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Jihar Abdulrahman Abba Jimeta, a safiyar yau a kasa mai tsarki bayan zuwa domin Umara.

Zaman makokin dai ya fara ne daga yau Litinin 18 ga watan Yuni zuwa Laraba 21 ga wata, kuma za a yi jana’izarsa a can kasa masallacin Harami da ke kasa tsarki wato Saudiyya da karfe biyu na ranar yau agogon Najeriya, kuma karfe hudu agogon Saudiyya.

Wata sanarwa mai dauke da sa-hannun kwamishina yada labaran Jihar  Ahmed Sajoh, ta ce gwamnan Jihar Muhammad Umar Bindow ya bukaci al’ummar Jihar su yi wa marigayin addu’ar neman gafara.

Abdulrahman Abba Jimeta ya rasu yana da shekaru 60, ya kuma bar mahaifinsa da mata guda da kuma ‘ya’ya 11.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,748 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!